Haka kuma kauyukan Mashama, Jena, Kalage, da kwaddi a karamar hukumar Zurmi yanzu haka barayi na cin karen su ba babbaka, da yawan wasu daga cikin 'yan gudun hijirar dakuke gani an kashe iya yensu da mazajensu kamar yadda wata 'yar gudun hijira ta shaidamin.
Duk da jibge Jami'an tsaro da gwamnatin tarayya ta yi a jihar Zamfara, al'ummar wannan yankin na kokawa da rashin kai dauki ko taimakon gaggawa na jami'an tsaron sojojin sama da aka turo domin kawo karshen kashe-kashe a jihar ta Zamfkoara.
Wani dattijo da nayi karo dashi a cikin 'yan gudun hijirar, malam Ibrahim lauwali yayi kirane ga gwamnatin taraiya da ta gaggauta kawomusu dauki a yankin Mashema dake karamar hukumar Zurmi domin wannan al'amari ya yi kamari matuka, inda yanzu haka 'yan gudun hijira sama da dubu biyar ne suke zaune a sansanoni da ban da ban na jahar ta zamfara.
27 Yuli 2018 - 16:54
Lambar labari: 903283
YAN BINDIGA SUN KWACE GARURUWAN INWALA,TUNGAR NASARA, GAMBIRO DAKE KARAMAR HUKUMAR ZURMI A JIHAR ZAMFARA: